Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya al'ummar Musulmi a ƙasar murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci. Cikin wani sako da shug...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya al'ummar Musulmi a ƙasar murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.
Cikin wani sako da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya buƙaci Musulmi da su koyi da ɗabi'un Manzon Allah Annabi Muhammad SAW da suka haɗa da hakuri da juriya da kuma karfin imani.
"A wannan lokaci da muke fuskantar matsaloli a ƙasar mu, ina so ku ci gaba da yin fata domin akwai nasara a gaba," in ji Tinubu.
Ya ce duk rintsi, shi da muƙarrabansa sai sun cika alkawuran da suka ɗauka wa ƴan Najeiya, duk da irin tarin wahalhalu ake ciki a yanzu.
Daga karshe ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da yin addu'a da kuma rokon Allah wajen samun saukin matsaloli da ƙasar ke ciki.
No comments