Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ce Gwamnatin Tarayya Tana Duba Yiwuwar Karin Albashi

  Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya tabbatarwa ma'aikatan Najeriya cewa gwamnati a shirye take domin sake duba albashin ma...

 


Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya tabbatarwa ma'aikatan Najeriya cewa gwamnati a shirye take domin sake duba albashin ma'aikatanta, a wani mataki na rage musu raÉ—aÉ—in cire tallafin man fetur.

Shugaban Majalisar, ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji da kuma ƴan majalisar wakilai na jihar.

Akpabio ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cire tallafin man fetur ne domin magance matsalar cin hanci da rashawa a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar.

Ya ce cire tallafin ne zai sa gwamnati ta fara yaki da rashawa gadan-gadan.

Akpabio ya kuma ce idan da ba a cire tallafin man fetur ba, Najeriya ba za ta iya tafiyar da harkokinta yadda ya kamata ba a cikin shekaru masu zuwa, inda ya ce za a sake duba batun albashin ma'aikata ne domin tabbatar da Æ´an Najeriya sun yi rayuwa yadda ya kamata.

No comments