Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sabuwar Shekarar Musulunci: Gwamna Lawal Ya Taya Musulmin Zamfara Murna

  Daga Muhammad A. Abubakar  Gwamna Dauda Lawal ya taya al’ummar Musulmin Zamfara murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445. Gwamnan y...

 


Daga Muhammad A. Abubakar 

Gwamna Dauda Lawal ya taya al’ummar Musulmin Zamfara murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.

Gwamnan ya taya al’ummar musulmin jihar, Nijeriya da ma duniya baki daya murnar shiga sabuwar shekara mai cike da albarkar Allah (SWT), inda ya bukaci da a ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da karuwar arziki a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Laraba, ya bukaci al’ummar Musulmi a fadin jihar da su dage da addu’a.

Ya ce: "sabuwar shekarar Musulunci tana wakiltar hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina. Wannan yana da matukar muhimmanci ga Musulunci da Musulmi.

“Hijirar ita ce farkon kalandar Musulunci da aka fi sani da ta Hijira.

“Muna da darasin da za mu koya, hijra ta nuna cewa mutanen da suke da imani, akwai saukin da zai zo bayan wahalhalu. Ya kamata jiharmu ta kasance cikin addu'o'inmu a koyaushe.

“Wani ma’anar Hijira shi ne cewa lokaci ne da aka samu hadin kan musulmi daga wurare daban-daban. Haka nan yana nuna tsarin 'yan uwantaka da daidaito na Musulunci.

“Ina so na yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga al’ummar jihar Zamfara da su hada kai wajen yaki da duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban jiharmu. Ina taya mu murnar sabuwar shekarar Musulunci 1445".

No comments