Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cutar Sankarau ya yi ajalin dalibai 20 a Yobe

Akalla dalibai 20 ne suka rasu a wasu makarantun sakandiren kwana da ke kananan hukumomin Potiskum da Fika da Fune a jihar Yobe sakamakon cu...



Akalla dalibai 20 ne suka rasu a wasu makarantun sakandiren kwana da ke kananan hukumomin Potiskum da Fika da Fune a jihar Yobe sakamakon cutar sankarau.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa bayanan da ta samu sun nuna an samu rashe-rashen ne a makarantun Government Science Technical College da Government Girls Science Technical College da kuma Federal Government Girls College dukkan su a karamar hukumar Potiskum.

Bayanan na nuna cewa da dama daga cikin karin wasu da cutar ta shafa suna asibiti suna karbar magani.

Kwamishinan Ilimin firamare da na Sakandare na jihar, Dr Muhammad Sani Idris ya tabbatar da barkewar cutar inda ya kuma amince da mutuwar daliban guda 20. Kamar yadda ya shaida wa jaridar da Daily Trust.

No comments