Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NLC ta dage zanga-zangar ranar Laraba

Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC ta sanar da janye zanga-zangar neman saukin tsadar rayuwa a ranar ta biyu wato ranar Laraba. Kungiyar ta c...



Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC ta sanar da janye zanga-zangar neman saukin tsadar rayuwa a ranar ta biyu wato ranar Laraba.

Kungiyar ta ce ta dage zanga-zangar ne ta ranar Laraba ne saboda ta sake bai wa gwamnati karin makonni biyu har zuwa 13 ga watan Maris domin biyan bukatunta.

A ranar Talata ranar farko ta zanga-zangar, daruruwan masu zanga-zangar neman saukin matsin rayuwa da ake ciki a Najeriya ne suka fantsama kan titunan biranen kasar bisa umarnin kungiyar ta kwadago.

Kungiyar kwadago dai ta yi kira da a yi zanga-zangar gargadi ta kwana biyu. To sai dai yanzu kungiyar ta sanar da janye zanga-zangar ta rana ta biyu wato ranar Laraba 28 ga watan Fabrairu.

No comments