An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kadun...
An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis.
Wani malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi wanda ya kubuta ya bayyana cewa ɗalibai 287 ne aka sace a makarantar.
Sani Abdullahi ya ce "A bangaren sakandare ɗalibai 187 ne suka bace amma bangaren firamare ɗalibai 125 da farko ba a gansu ba amma daga bisani guda 25 sun dawo."
Malamin wanda ya bayyana hakan lokacin da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ziyarci makarantar domin gani da ido yadda lamarin yake , ya kara da cewa "na shigo makaranta misalin karfe 7:45 sai na shiga ofishin principal kuma sai ya ce min in waiga baya, ina juyawa sai naga 'yan bindiga sun kewaye makarantar".
"Mun ruɗe bamu san inda zamu ba, kafin da suka tafi damu daji sai muka canza hanya," in ji Sani Abdullahi.
Malamin makarantar ya ce 'yan bindigar sun kashe mutum daya.
Yaran da lamarin ya rusta da su shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15.
Ya bayyana cewa ana cikin wani hali na fargaba tun bayan sace daliban a safiyar Alhamis.
Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce “Babu wani gida a Kuriga wanda wannan abin bai shafe shi ba”.
Gwamna Uba Sani ya ziyarci makarantar
Gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin kubutar da daliban inda ta yi alkawarin za ta sake gini ofishin 'yan sanda a garin a yunkurin ta na kare rayukar al’umma.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci makarantar ta kauyen Kuriga da 'yan bindiga suka sace dalibai, ya kara da cewa ba zai huta ba har sai an kubutar da yaran gaba dayansu.
Ko a watan Janairun shekarar nan, wasu ƴan bindiga sun shiga ƙauyen na Kuriga, inda suka kashe shugaban makaranta tare da sace matarsa.
Kuriga ƙauye ne da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, yankin da ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan ƴan fashin daji.
A shekarar 2023 ƴan bindiga sun kai hari kan sojojin da ke sintiri a kan hanyar tare da ƙona mota mai sulke.
Sace-sacen ɗalibai irin wannan na tuno wa al'ummar Najeriya da satar ƴanmatan makarantar sakandaren Chibok da ke jihar Borno, inda a daren 15 ga watan Afrilun 2014 mayaƙan Boko Haram suka kai farmaki a makarantar tare da sace ɗalibai sama da 200.
No comments