Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya yi tur da hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan makarantu a...
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya yi tur da hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan makarantu a jihar Kaduna.
Shugabar Asusun a Najeriya, Cristian Munduate, ta nuna rashin jin daɗinta sakamakon harin, inda ta ce ya kamata kowane yaro ɗan Najeriya ya samu damar koyon ilimi cikin kwanciyar hankali.
Ta ce ya kamata a ce makarantun su zama wurin koyo da ci gaba, ba wai wuraren fargaba da tashin hankali ba.
Cikin sanarwar, "na kaɗu matuƙa da rahotannin satar ɗalibai a jihar Kaduna. Ƙaruwar irin waɗannan sace-sace a sassan ƙasar na nuna wata matsala da ke buƙatar a gaggauta ɗaukan mataki daga dukkan matakan gwamnati da kuma su kansu al'umma." in ji Munduate.
Unicef ya kuma buƙaci a gaggauta ɗaukan matakin tabbatar da maido da yaran da aka sace, inda kuma ya yi kira ga hukumomi da su ɗauki ƙwararan matakai don tabbatar da tsaro a sassan Najeriya.
A cewarta, ya zama dole a tabbatar wa ɗalibai da malamansu tsaro domin makarantu su iya sauke nauyinsu na zama wuraren samun ilimi da ci gaba.
A shekarun baya-bayan nan ana samun ƙaruwar satar ɗalibai a makarantu a sassa daban-daban na Najeriya.
No comments