Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Muna Cikin Bala'in Rashin Ƴaƴanmu Da Aka Sace A Kuriga – Iyaye

Ɗaya daga cikin iyayen ɗalibai 287 da ƴan bindiga suka sace daga wata makarantar Firamare a Kuriga da ke jihar Kaduna ta yi kira...


Ɗaya daga cikin iyayen ɗalibai 287 da ƴan bindiga suka sace daga wata makarantar Firamare a Kuriga da ke jihar Kaduna ta yi kira ga hukumomi su yi duk abin da ya kamata domin kuɓutar da yaran.

A hirarta da BBC, mahaifiyar wadda har yanzu bata ga 'yarta ba, ta bayyana yadda ta rabu da ƴartata gabanin a kai harin da aka yi garkuwa da su.

"Ta fita da larura, jikinta ba ta jin daɗi, na kora ta a kan ta tafi makaranta kar ta yi latti ko karyawa ba ta yi ba, ƴan bindiga suka kawo mamaya, sun mamaye makarantar nan,"

"Ba ta inda yaranmu za su fita sai wanda Allah ya tseratar, sun bar mu cikin halin ibtila'i, muna hangen ƴaƴanmu ana kora mana su, mun yi kuka, Uba Sani ka taimaka mana." in ji mahaifiyar.

Ta ce akwai matsalar rashin tsaro a Kuriga gami da yunwa da suke fama da ita a yankin.

A cewarta, makarantar ce kaɗai abin da suke cin moriya daga gwamnati.

Cikin shesshekar kuka ta ce ƴan bindigar "sun hana a yi noma, sun hana a yi kiwo, an bar mu cikin talauci kamar ba ma tare da gwamnati." kamar yadda ta faɗa.

Ita ma wannan mahaifiyar ta bayyana yadda lamarin ya faru "ina zaune a cikin gida, kawai sai na ji ƙarar bindiga, sai aka ce ɓarayi ne, sun tattara mana yara sun tafi da su.".

Ta nemi hukumomi su kai musu ɗauki ganin yadda mazajensu suke kwana a tsaye inda suke kai kawo domin tabbatar musu da tsaro.

A cewarta, yankin Kuriga na fama da matsalar rashin jami'an tsaro, abin da ke jefa rayuwarsu cikin barazanar hare-haren ƴan bindiga.

No comments