Hukumomi a Uganda sun haramta sayar da nama a Kamfala babban birnin ƙasar, a wani mataki na hana yaɗuwar wata cuta da ke kama ko...
Hukumomi a Uganda sun haramta sayar da nama a Kamfala babban birnin ƙasar, a wani mataki na hana yaɗuwar wata cuta da ke kama kofato da kuma bakin dabbobi.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito ma'aikatar noma da kiwo ta ƙasar na cewa "An haramta shiga da fitar da dabbobi cikin birnin, da ma wucewa da su, har sai yadda hali ya yi.''
Ma'aikatar ta ce "An rufe duk wata kasuwar dabbobi da mayanka da kuma sauran wuraren sayar da dabbobin da nama na cikin birnin."
Hukumomin sun ce za su yi aiki tare da jami'an da suka dace wajen tabbatar da bin dokar, duk da cewa akwai rahotonannin da ke cewa wasu shagunan siyar da nama suna aiki a birnin.
Cutar da aka gano mai kama kofato da bakin dabbobi na yin barazana ga lafiyar jama'a.
No comments