Ƙungiyar Amnesty International ta ce sace fiye da ƴan gudun hijira a jihar Borno da ɗalibai ɗari biyu da tamanin da bakwai da ma...
Ƙungiyar, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a ta hannun shugabanta a Najeriya, Isa Sanusi, ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da mutanen da aka sace domin haɗa su da iyalansu.
A cewar ƙungiyar, dole ne hukumomi su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yawaitar sace-sacen da ake yi a sassa da dama na Najeriya tare da gabatar da sakamakon binciken ga al'umma sannan su tabbatar an hukunta waɗanda aka samu da hannu a garkuwa da mutane.
Amnesty ta ce, "sace-sacen mutane da dama a baya-bayan nan ƙarara sun nuna cewa shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa ba su da tsayayyen tsari na kawo ƙarshen miyagun laifukan ƴan bindiga da ke cin karensu babu babbaka a sassan jihohin Najeriya. Duk matakan tsaron da shugaba Tinubu da gwamnatinsa ke aiwatarwa ba sa tasiri," in ji Isa Sanusi.
"Ganin yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa a Najeriya a yanzu, a bayyane take cewa batun kare rayuwa da dukiyoyin al'umma ya na ƙasa cikin jerin abubuwan da gwamnati ta sa a gaba. Bai kamata a ƙyale mutane su zauna cikin fargaba da tsoron hari da garkuwa ba.
Yawan gazawar hukumomin Najeriya wajen kare mutane abu ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba kuma dole ne a kawo ƙarshen sa," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Amnesty ta kuma yi kira da a tabbatar da waÉ—anda ke da nauyin samar da tsaro a yankunan da aka yi sace-sacen jama'a su yi bayani kan gazawar da ta jefa rayuwar É—aruruwan mutane cikin haÉ—ari.
A ranar Alhamis ne wasu ƴan bindiga suka kai hari kan wata makarantar Firamare a Kuriga da ke jihar Kaduna inda suka sace ɗalibai kimanin 287 da malaminsu guda ɗaya, sai dai malamin ya samu kuɓuta sai kuma ɗalibi guda da ya mutu.
No comments