Daga Hussaini Yero Matar gwamnan jhar Zamfara, Hajiya Huriya Dauda ta yaba wa Kungiyar NLC tsawon watanin da suka yi a mulki ba ...
Daga Hussaini Yero
Matar gwamnan jhar Zamfara, Hajiya Huriya Dauda ta yaba wa Kungiyar NLC tsawon watanin da suka yi a mulki ba su taba shiga yajin aiki ba.
Hajiya Huriya Dauda ta bayyana haka ne a wajen taron tunawa da ranar Mata da duniya da Kungiyar NLC mata suka shirya a Gusau babban Birnin Jihar Zamfara.
Matar gwamnan ta jinjinawa Kungiyar NLC matan da suka shiga sahun wajan amsa kiran Majalisar dinkin duniya da ta ayyana Ranar Mata ta duniya dan yin bukukuwan da kuma yadda mata za su magance matsalolin su na rayuwa.
Akan haka ne Hajiya Huriya Dauda ta tabbatar wa ma'aikatan Jihar Zamfara cewa, gwamnatin mai gidanta gwamna Dauda Lawal, tana da shiri na musamman akan jin dadin ma'aikata wanda ta ce su shaida ne akan haka; "don a ƙarshen shekara da ta gabata gwamatin Zamfara taba ma'aikatan jihar kyautar albashi don ganin sun shiga cikin sabuwar shekara lafiya ba tare da baduka akan su ba".
"Kuma yanzu haka gwamnati na nan na shirin tsare-tsaren ci gaban ma'aikatanta kowanne fanni a wannan jihar ta mu."
A nata jawabin shugabar Ƙungiyar NLC matan ta Jihar Zamfara, Kwamared Binta Yusuf Gusau, ta bayyana jindadin ta na halartar Uwar gidan gwamnan Zamfara Huriya Dauda taron da suka shirya na tunawa da ranar Mata ta duniya a Sakatariyar Hukumar ta jiha dake Gada biyu Gusau babban birnin Jihar.
Kwamared Binta Yusuf ta bayyana nasarorin da Ƙungiyar ta samu da kuma kalubalen da ta ke fuskanta musamman na ganin ta wayar da kan mata bidar Ilimi da sana'a dan dogaro da kai.
Kuma ta yi kira ga gwamnati jihar Zamfara da ƙara duba mata wajen ba su manyan mukamai na gwamnati da na siyasa dan sune ginshikin samun kowace nasara a jihar ar da Ƙasa baki daya.
A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar NLC na jiha Kwamared Sani Haliru ya bayyana godiyar sa ga Uwargidan gwamna Dauda Lawal, Hajiya Huriya akan amsa gayyatar wannan gagarimin biki.
Kuma mu ma'aikatan Jihar Zamfara, shaida ne akan abin da Uwar gidan gwamna ta fada na tsare-tsaren ci haban ma'aikata jihar. "Kuma Hausawa na cewa, Juma'ar da za ta yi ƙarko tun a Laraba ake ganeta, to mu ma'aikatan jihar Zamfara tun a Litinin muka gane tamu, don yanzu ne Allah ya kawo shugaba Mai son ci gaban ma'aikata ta kowanne sashe. Don haka mu babu abin da zamu ce illah godiya ga Mai girma gwamna Dauda Lawal da Uwar gidans don duk wani koke da muke da shi muka kai gaban gwamna Dauda yana magance mana shi", in ji shi.
"Kuma akan haka ne muke tabbatar wa Uwargidan gwamna Dauda cewa, tsakanin mu da Gwamna sai godiya da addu'a dan samun nasara gwamnatin sa akan kudirinsa na ci gaban jihar Zamfara".
No comments