Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RAMADAN: Ɗan Majalisar Tarayya Ya Raba Kayan Abinci Tare Da Makudan Kuɗaɗe Ga Mutum Sama Da Dubu Uku A Mazaɓarsa

Daga Muttaqa Kumasy A ranar 15-3-2024 an shiga rana ta shida da Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Suleja, Gur...

Daga Muttaqa Kumasy

A ranar 15-3-2024 an shiga rana ta shida da Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Suleja, Gurara da Tafa yake rarrabawa al'ummarsa kayan abinci, hade da kuɗaɗe domin samun sauƙin gudanar da ibadar azumi. 

Ya fara rarraba abincin ne tun ranar jajiberin azumi, inda a wannan rana aka shiga rana ta shida, washegari aka ci gaba. 

Ana rarraba abincin ne cikin tsari, ba tare da hayagaga ba. 

Abincin da ake rabawa sun haɗa da; shinkafa mai nauyin Kilogiram 50, da kuma 25, sai mai nauyin Kilogiram 10 da kuma 5, haɗe da gero, Indomie, Madara, ƙwai da kuma mai. 

Sannan kuma ya rarraba kuɗaɗen yin cefane. Tsarin rabon abincin, kowacce mazaɓa ana bata, ƙungiyoyin siyasa da ƙungiyoyin Unguwanni ma ana ba su, ƙungiyoyin addinai, Limamai, Dagatai, da kuma masu buƙata ta musammam (Guragu da makafi) da sauran jama'a marasa galihu duk suna ci haba da amfana da tallafin abincin da Ɗan Majalisar yake rabawa a duk ilahirin ƙananan Hukumomin Suleja, Gurara da Tafa.  

Haka zalika duk a cikin watan azumin nan, Hon. Adamu Tanko Lokoja ya ba ƙungiyar Izala reshen Tafa N300,000 don hidimar addini. 

Ita Kuma ƙungiyar Fityanul Islam sun rabauta da N100,000 da kuma kayan abinci. 

Ya Kuma ba ƙungiyar Jama'atul Nasrul Islam N100,000 tare da kayan abinci. 

Hon. A.T.L ya ba ƙungiyar Izala reshen Madalla N200,000, waɗannan ayyukan alkhairi duk yanayin su ne a cikin watan azumin nan.

Ga wasu daga cikin hotunan rabon da wakilinmu ya turo mana.

No comments