Daga Umar Idris, Zariya Kamar yadda kafafen yada labarai ke tabbatar da cewa Shehin Malamin nan wanda yake rike da mukamin shuga...
Daga Umar Idris, Zariya
Kamar yadda kafafen yada labarai ke tabbatar da cewa Shehin Malamin nan wanda yake rike da mukamin shugaban rundunar Hisba ta jihar kano wato Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye aikinsa a ranar Juma'a 1/2/2024 wanda gwamnatin Kano ta bashi don kawo kyakkyawan tsari a sashen Hisba karkashin gwamnan jihar ta Kano Kabir Abba Yusuf Gida-gida.
Bisa hakan ne wakilinmu ya zanta da mataimakin mai tsawatarwa a majalisar jihar Kaduna kuma shugaban kwamitin addini na majalisar jihar Kaduna wakilin mazabar gundumar Basawa a karamar hukumar Sabon Gari wato Sheikh Honorabul Jamilu Abubakar Albani Samaru ta wayar S'salula.
Sheikh Abubakar Jamilu Albani Samaru shi ne Sakataren majalisar malamai na kungiyar Jamatul Izalatul Biddi'a wa'Ikamatussunah ta ƙasa kuma matashin ɗan siyasa a shiyya ta ɗaya (zone one) a jihar Kaduna.
Honorabul Albani ya shaidawa wakilinmu cewa wannan mataki ya yi tsauri da yawa ya ce, a gaskiya bai mishi dadi ba musamman yadda al'umma suke matukar farin ciki da sa rai da cewa za a sami sauyi mai tsafta a hukumar ta Hisban baki daya musamman ganin Sheikh Aminu Daurawa a matsayin shugabanta mai cikaken iko.
Sheikh Albani ya ce, duk da ba jam'iyyarsu ba É—aya ba amma zuwan Sheikh Daurawa hukumar Hisba jihar kano ta kara samun farin jini sosai a bangaren siyasa da zamantakewar zamani.
Tuni Dan majalisar ya yi roko ga gwamnan jihar ta Kano da sauran masu fada aji na jihar Kano su yi wa Allah da Annabinsa su sanya baki a cikin wannan lamarin don a sami matsaya mai kyau ga al'umma.
Kuma Dan majalisar ya bayar da shawara cewa gwamna ya tura manyan malamai su tattauna da Sheikh Daurawa akan wannan lamarin don shawo kan dukkan matsalolin dake cikin hukumar ta Hisban ba tare da bata wani lokaci ba musamman a matsayinsa a Uba a wannan jihar mai Albarkar.
Hakazalika Dan majalisar ya yi kira ga Sheikh Daurawa cewa ya yi hakuri haka hanyar Allah take kuma duk mai son kawo gyara to zai fuskanci kalubale kala-kala musamman yadda jihar kano take a Nijeriya da Afrika baki daya.
Karshe Ɗan majalisar ya yi fatan dukkan ɓangarorin biyu za su yi hakuri su kawo hanyar da za a sami mafita gami da fahimtar juna don ci gaban jihar Kano da ƙasa baki daya.
Babban kwamandan Hukumar Hisba Na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana sauka daga mukamin sa na babban Kwamandan Hisba na Jihar Kano ne a wata sanarwa da ya fitar cikin wani faifan Bidiyo mai motsi da ya bayyana da safiyar Ranar Juma'a
Aminu Daurawa ya bayyana cewa yana Kaduna yana halartar Tltaron da ake gudanarwa tare da majalisar dokokin jihar jan kokarin samar da dokar tabbatar da yin gwaji kafin aure kamar yadda wasu jihohi Slsuka gabatar a jihohinsu. Ya ce kwatsam sai yaji wasu bayyanai na ta fita inds Gwamna ya nuna ɓacin ransa kan wasu matakai da Hukumar ta Hisba ta dauka domin kyautata tarbiyyar al'umma.
Aminu Daurawa ya ci gaba da cewa a nasa bangaren ya yi bakin kokarinsa wajen tattaunawa da masu sanaa'ar shirya fina-finai da Æ´an wasan TikTok wanda ya ce a aljihunsa da abokan aikinsa suka haÉ—a kudaden da aka bai wa 'yan TikTok domin sayan Data duk domin su tsaftace abubuwan da suke yi, amma dai wasu sun ci ga da abin da suke yi wanda hakan yasa Hisba ta dauki wasu mataki don kawo gyara.
Daga nan sai Aminu Ibrahim Daurawa ya baiwa Gwamnan hakuri bisa abin da ya yi wanda a zaton sa kokarin umarni ne da kyawawan aikin alkhairi ne da kuma hani ga mummunan aiki, kamar yadda addinin Islama ya koyar don haka ya ce a wannan rana ta Juma'a 1/3/2024 ya sauka daga wannan kujera na kwamandan Hisba gaba daya. Kuma ya bai wa gwamna hakuri a nan take.
No comments