Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Ɓata Gari Suka Daka Wa Motar BUA Wawa A Kan Hanyar Zariya

Wasu ɓata gari sun daka wa wata motar dakon kayan abinci ta Kamfanin BUA wawa a Unguwar Dogarawa da ke babban titin Zariya zuwa ...

Wasu ɓata gari sun daka wa wata motar dakon kayan abinci ta Kamfanin BUA wawa a Unguwar Dogarawa da ke babban titin Zariya zuwa jihar Kano.

Ɓata garin dai kamar yadda ganau ya shaida wa wakilinmu cewa sun ɗauke katon-kato na taliya da motar ke ɗauke da su da yammacin ranar Juma’a.

Ɓata garin sun kai wa motar hari ne da misalin ƙarfe 3 na rana lokacin da direban motar ya tafi kama ruwa don yin ibada.

Wani ganau ya shaida wa majiyarmu cewa, direban ya tsaya ne don kama ruwa don yin sallah.

Nan take, suka gane cewa taliya ce a cikin motar suka afka mata tare da wawushe duk abin da suka ci garo da shi a cikin motar.

Ganau din ya ƙara da cewa ɓata garin sai da suka wawushe dukkan katan-katan ɗin taliyar da motar ke ɗauke da shi kafin daga bisani kowa ya tsere da abin da ya samu gida.

Wakilinmu ya ruwaito cewa daga baya dai jami’an tsaro sun kawo ɗauki domin ɗaukar matakin gaggawa

Ya zuwa haɗa wannan labarin dai jami’an tsaro yankin sun cika hannu da wasu daga cikin bata garin. Amma bayanai sun ce an tafka asara mai yawa.


No comments