Daga Awwal Umar Kontagora Ƙungiyar manoma ta 'All Green Agro-Field Farmers Processors and marketers Association (AGAFPAMA)...
Daga Awwal Umar Kontagora
Ƙungiyar manoma ta 'All Green Agro-Field Farmers Processors and marketers Association (AGAFPAMA)' ta ƙasa reshen jihar Neja ta sha alwashin marawa gwamnati baya wajen bunƙasa harkar noma.
Sakataren ƙungiyar ta ƙasa kuma shugaban ƙungiyar a jihar Neja, Ambassada Nura Hashim (Tallafin Bosso Ƙarami) ne ya bayyana hakan a lokacin da aka rantsar da shugabannin ƙungiyar reshen jihar Neja a Sakatariyar ƙungiyar da ke Okada road cikin garin Minna.
Amb. Nura, ya ci gaba da cewar "idan muka haɗa kai, tabbas za mu ciyar da jihar nan gaba, noma shi ne ƙashin bayan ci gaban kowacce al'umma musamman wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa, hanya ce ta tallafawa rayuwar ɗan Adam wajen tsayuwa da ƙafarsa. Za mu ciyar da iyalan mu, za mu taimaki rayuwar mu, kuma zamu taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin mu", in ji shi.
Ya ci gaba da cewa; "Manufar wannan ƙungiyar shi ne bunƙasa tare da inganta harkar noma ta hanyar ƙarfafa manoman na asali, za mu tabbatar duk wani hanyar ci gaban noma, ta hanyar haɗa hannu da gwamnati da masu ruwa da tsaki don bunƙasa harkar noma a jihar nan da ƙasa baki ɗaya".
Amb. Nura Hashim, ya yabawa gwamnatin jiha da ta tarayya kan yunƙurin farfaɗo da shirin noma a ƙasar nan.
"Shirin bunƙasa kasuwancin abinci, zai taimaka wa manoman mu wajen samun sauƙin saye da sayar da kayan abinci. Manoman mu da cibiyoyin bunƙasa harkar noma, na buƙatar kasuwanci mai Inganci. Za mu samar da kasuwanci mai Inganci, da samar da hanyoyin fitar da kayan abinci waje", ya jaddada.
Tallafin Bosso, ya ci gaba da cewar ƙungiyar za ta tabbatar ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnati da kuma masu zaman kansu, musamman domin tabbatar da cewar shirin gwamnatin jiha na bunƙasa harkar noma a ƙarƙashin babban manomin jiha, Manomi Umaru Mohammed Bago na ganin jihar ta tserewa tsara a ɓangaren noma.
"Musamman don ganin membobin mu sun samu tallafi, da gudunmawar kayan aiki ta yadda zamu samu sauƙin zamanantar da ɓangaren noma don ƙaruwar manoman jihar Neja. Mata da matasa ba ƙashin yarwa ba ne, kuma ɓangaren noma na buƙatar gudunmawar matasa, zamu tabbatar mun ƙarfafa guiwar matasa wajen kasuwancin anfanin gona, mu tallafa wa mata dom samun tsayuwa da ƙafarsu tare da tabbatar sun zama jagorori a wannan ɓangaren", ya tabbatar.
A bayaninsa, Sakataren gudanarwa na ƙungiyar ta ƙasa, wanda ya wakilci shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Alhaji Ibrahim Mai Jama'a Leme, ya yabawa shugabancin ƙungiyar ta jihar, inda ya bayyana cewar kusan dukkanin waɗanda zaɓo su jagoranci tafiyar nan, shugabannin ne da ke jagorancin ƙungiyoyin manoma daban daban, wanda bisa wannan yunƙurin za mu ce jihar Neja ita ce jiha ta farko a yankin arewa ta tsakiya da aka rantsar zuwa yanzu kuma suka kafa harsashin tafiya mai Inganci.
"Wannan tafiyar ta AGAFPAMA tazo daidai da ƙudurin gwamnan Neja, babban manomin jiha, Umaru Mohammed Bago na dawo da martabar noma wanda kusan a Afrika yanzu ba na jin akwai gwamnatin jiha da za ta haɗa kafaɗa da jihar Neja", in ji shi.
Barista Isah Ibrahim Alhaji ne ya jagoranci rantsuwar, wanda kwamishinan ma'aikatar gona, Malam Salihu Bawa Bosso ya samu wakilci, yayin da sauran ɓangarorin hukumomin harkar gona ba a bar su a baya ba.
Kwamishinan a saƙon da ya aiko, ya yi kira ga sabbin shugabannin da su haɗa kai don yin aiki tare, inda ya ce haɗa kai shi ke sa a cin ma burin ganin jihar nan ta bunƙasa a harkar noma, kuma manoma su amfani ƙudurin gwamnatin na tallafa masu.
Bawa Bosso, ya nemi ƙungiyar da ta tabbatar ta yi rajista da ma'aikatar kula da harkar noma, hakan ne zai ba su damar samun haɗin kai da gwamnatin jiha don yin aiki tare da tabbatar da bunƙasar ɓangaren noma a jihar Neja.
Alhaji Ibrahim Leme, ya bayyana cewar yanzu haka a matakin ƙasa, ƙungiyar ta yi nisa wajen haɗa kai da babban bankin CBN wajen bunƙasa noman rogo, alkama, riɗi da sauran su, nan bada jimawa 'ya'yan wannan ƙungiyar za su shaidi irin huɓɓasar da uwar ƙungiya ta ƙasa ke yi don amfanan manoman ƙasar da kuma zama tsani wajen ganin dukkanin ƙudurce ƙudurcen gwamnati ya kai inda ake buƙata.
Alhamdu lillah muna maraba da wannan kungiyar domin kuwa shugabanta na jahar Niger mutumne jajirtacce Wanda ke kokarin kawo cigaba ga al'umma.
ReplyDelete