Daga Hassan Ibrahim A ranar juma'a 11 ga wannan wata da muke ciki ne Allah ya yi wa Aminu Yusuf Giɗaɗo rasuwa, kashiya na ...
Daga Hassan Ibrahim
A ranar juma'a 11 ga wannan wata da muke ciki ne Allah ya yi wa Aminu Yusuf Giɗaɗo rasuwa, kashiya na ƙaramar hukumar Maƙarfi kuma ƙani ga shugaban ƙaramar hukumar Maƙarfi, Hon. Garba Muhammad Sabon Gari, sanadiyyar haɗarin mota akan hanyar sa ta dawo wa Kano dai dai Kwanar Ɗan Gora aka kuma gudanar da jana'izar sa a filin idi na cikin garin Maƙarfi bayan sallar la'asar.
Sallar jana'izar marigayin ya samu halartar al'umma da dama.
Al'umma na cigaba da miƙa ta'aziyyar su ga ƴan uwa da abokan arziki da kuma iyalan marigayin.
Marigayin ya rasu ya bar mace ɗaya da ƴaƴa huɗu, mata uku namiji ɗaya.
Muna addu'ar Allah ya jikansa, ya gafarta masa kuma yasa Aljannah firdausi ce makomar sa.
No comments