Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ina Da Ƙwarin Guiwar Duk Jam'iyyar Da Ta Ci Hukumar Zaɓe Za Ta Ba Ta Abinta, in ji Ɗan Takarar SDP

Daga Awwal Umar Kontagora Biyo bayan sanarwar hukumar zaɓe ta jihar Neja kan dakatar da miƙa sunayen 'yan takarkarun shugaba...

Daga Awwal Umar Kontagora

Biyo bayan sanarwar hukumar zaɓe ta jihar Neja kan dakatar da miƙa sunayen 'yan takarkarun shugabancin ƙananan hukumomin jihar Neja da hukumar ta yi yammacin Alhamis ɗin makon nan bisa ƙwararan dalilai.

Jaridar Madogarar Labarai, ta zanta da ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Kontagora a ƙarƙashin jam'iyyar SDP,  Hon. Garba Ibrahim Madara.

A tattaunawar, ya bayyana cewar babban manomin jiha, Gwamna Umaru Mohammed Bago adalin gwamna ne, wanda ya goge kuma.kwararre a tafiyar siyasa da har ya samu kambun girmamawa daga kasa mai tsalki wanda aka baiwa sanfurin karramawa ta makullin ka'aba. Da wannan dalilin na ke kyautata cewar gwamnatin ba za ta goyi bayan murde zaben yan takarkarun da suka ci zabe a jam'iyyun adawa ba.

Hon. Madara ya cigaba da cewar dangane da shirye shiryen hukumar zabe ta jiha a yanzu, ban tsammani akwai kudurin coge ko murdiyar zabe, duk da cewar wadanda aka baiwa jagorancin hukumar a yanzu sababbi ne, akwai ina da kwarin guiwar akwai mutanen kirki a cikin su.

Matsalar da aka samu tun farko, gwamnati ta bada damammaki ta yadda al'umma zasu ci moriyar mulkin dimukuradiyya, amma kusan wadanda aka baiwa mukaman kwamishinoni da yan siyasa ba ne, suka watsar da wadanda suka wahala a siyasar suka koma rabawa yan uwansu da yan uwan matansu gurabun da gwamnati ta bayar dan cin moriyar yan siyasar.

Idan Allah ya ba mu nasara, muna da tsare tsaren farfado da tattalin arzikin karamar hukumar ta hanyar samar da gurabun ayyuka ga matasa musamman a bangaren noma da kasuwanci.

Yau duk wanda ya dubi kudurin gwamnatin Umaru Bago, kuduri ne na farfado da bangaren noma, wanda tuni muna da gogewa da sanin makaman aiki a wannan bangaren, a kiwon kaji kawai za mu iya samar da gurabu sama da dari biyar ga matasa, noman yazawa, da kadanya wanda yana daga cikin bukatun kasuwan duniya, za mu tabbatar manoman mu sun anfana da wannan damar.

Saboda haka, kudurin shi ne dawo da martabar noma da kasuwanci wanda su ne suka kafa kasar Kontagora, mun shahara a noman auduga, gyada da makamantansu, za mu kasance da kwararrun masana aikin gona ta yadda za mu tabbatar ban cin samar da gurabun ayyuka na dogaro da kai, mun yi anfani da wannan damar wajen samar da hanyoyin kudaden shiga ga gwamnati ta yadda za a rage dogaro da kudaden da ke shigowa daga aljihun gwamnatin tarayya.

Hon. Garba Madara, ya yi kira ga mata da matasa da su yi watsi da duk wani yunkurin tada zaune tsaye su tabbatar a lokacin zabukan kananan hukumomi sun zabi cancanta, muddin suka ba shi goyon baya kudurinsa shi ne al'ummarsa.
Gwamnatin da za mu kafa a karamar hukumar Kontagora gwamnati ce ta kowa da kowa wadda za a hada wajen ceto tattalin arzikin karamar hukumar da tabbatar da samun ingantaccen tsaro ta yadda manoma zasu samu kwarin guiwar mayar da hankalin su ka'in da na'in a harkar noma.

Ba mu da wata damar da ta wuce anfani da katin kuri'ar mu wajen zaben mutane nagartattu da mu ka yi ammanar da zasu tabbatar da baiwa marada kunya, inji shi.

No comments