Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar AIRLIN Ta sha alwashin Dawo Da Zaman Lafiya A Filato

Daga Zubairu M. Lawal Ƙungiyar AIRLIN, wadda ke fafutukar gyaran dabi’u da inganta haɗin kan ’yan Nijeriya, ta kaddamar da ofish...

Daga Zubairu M. Lawal

Ƙungiyar AIRLIN, wadda ke fafutukar gyaran dabi’u da inganta haɗin kan ’yan Nijeriya, ta kaddamar da ofishinta na biyar a jihar Filato a ranar Talata.

Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen faɗaɗa ayyukan ƙungiyar a jihohi 19 na Arewacin Nijeriya, inda aka riga aka buɗe ofisoshi a Bauchi, Nasarawa, Katsina, da Niger.

A yayin bikin kaddamarwar da aka gudanar a birnin Jos, shugaban ƙungiyar, Alhaji Mohammed Gamawa, ya bayyana cewa manufar AIRLIN ita ce wayar da kan ’yan kasa kan haƙƙoƙinsu da nauyin da ke kansu wajen gina kasa mai zaman lafiya da adalci.

“Muna da burin ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan Najeriya, ƙarfafa bin doka, da ilmantar da jama’a su fahimci muhimmancin yin zaɓe bisa gaskiya, ba bisa son zuciya ba,” in ji Gamawa.

Ya ƙara da cewa fahimtar haƙƙin ɗan ƙasa da bin doka suna tafiya hannu da hannu wajen gina ƙasa mai nagarta. “Zamu ci gaba da taimakawa matasa wajen guje wa miyagun kwayoyi, fadakar da direbobi kan hadurran tukin ganganci, da kuma wayar da kan jama’a su kauce wa siyasar kuɗi,” in ji shi.

Bikin ya kuma haɗa da naɗa jami’an kula da jiha da ƙananan hukumomi 18 da za su taimaka wajen aiwatar da ayyukan ƙungiyar a fadin jihar Plateau.

Alhaji Gamawa ya ce ƙungiyar na da niyyar kafa ofisoshi a dukkan jihohin Arewa don kara kusanci da jama’a, tare da samar da sabis na musamman, ciki har da yin kati na dan ƙasa kyauta har a gidajen mutane.

Taron ya fara da jajantawa al’ummar da rikicin tsaro ya shafa a wasu sassan Plateau, musamman harin ’yan bindiga da ya afku a ranar Litinin da ta gabata.

A halin yanzu, AIRLIN na da burin samar da  mambobi sama da miliyan bakwai (7) a fadin Najeriya, kuma tana ci gaba da karfafa gwiwar su wajen zama wakilai na gaskiya domin samar da  zaman lafiya a cikin al’umma.

No comments