Daga Ammar M. Rajab Kakakin Majalisar Wakilai, Honorabul Tajudeen Abbas, GCON, ya naɗa tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Gar...
Daga Ammar M. Rajab
Kakakin Majalisar Wakilai, Honorabul Tajudeen Abbas, GCON, ya naɗa tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Injiniya Muhammad Ibrahim Usman, a matsayin Babban Mai Taimaka Masa kan sha'anin Dokoki.
An tabbatar da naɗin ne a cikin wata sanarwa da aka aika wa tsohon shugaban ƙaramar hukumar, inda jaridar MADOGARA ta samu kwafinta.
Bayan sanarwar, sakonnin taya murna sun cika a kafafen sada zumunta, inda 'yan uwa, abokai da masoya ke murnar wannan naɗin inda suka bayyana a matsayin wanda ya dace da cancanta.
Injiniya Usman, wanda aka san shi da jajircewa da gudummawa wajen ci gaban al'umma a lokacin da yake shugabantar ƙaramar hukumar Sabon Garin, ana sa ran zai yi amfani da ƙwarewarsa da gogewarsa a sabon muƙaminsa a Majalisar Tarayya.
No comments